✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Katsinawa sun yi wa Buhari bore da ihun ‘ba ma yi’

Wasu mazauna a Jihar Katsina sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari bore dangane da yadda aka shiga tsaka mai wuya kan wa’adin amfani da tsofaffin…

Wasu mazauna a Jihar Katsina sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari bore dangane da yadda aka shiga tsaka mai wuya kan wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudi a kasar.

Mazaunan sun yi wa Buhari boren ne a yayin ziyarar aiki da ya kai birnin na Dikko a ranar Alhamis.

Zanga-zangar dai ta gudana ne a Kofar Kaura, Kofar Kwaya da kuma hanyar Yahaya Madaki a cikin birnin Katsina.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun kona tayoyi a kan titi tare da jifan wasu daga cikin tawagar motocin shugaban kasar da duwatsu.

Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun fusata ne saboda karancin man fetur, hauhawar farashi da matsalar rashin tsaro.

A zantawar Aminiya da wani matashi da lamarin ya faru a kan idonsa, ya bayyana cewa, “Shugaban Kasar na barin Kofar Kaura, wasu matasa suka soma ihun ‘Ba ma yi’.

“Suka fara kona tayoyi da jefa duwatsu kan wasu jami’an tsaro, wadanda su kuma suka mayar da martani ta hanyar harba barkonon tsohuwa.

“Sunana Mustapha Muhammad Boss. Abin da ya faru shi ne bayan Shugaba Buhari ya kaddamar da gadar kasan, wasu matasa wadanda ba mu san ko daga ina suka fito ba, suka fara ihun ‘Ba mu yi’, suna jifar jami’an tsaro da wasu motocin da ke dauke da alamun APC, sannan da kuma kona tayoyi.”

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya musanta aukuwar duk wadannan lamari.

“Ko kadan ba a yi wa Shugaban Kasa ihu ba, sannan ba zanga-zangar da aka yi.

“Mutanen jihar sun fito kwan su da kwarkwatar su sun tarbi Shugaban Kasa,” a cewar SP Gambo.