✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku yi hattara da romon bakan Atiku —Tinubu ga ’yan Najeriya

“Obasanjo ya rubuta cewa babbar katobara ce, “zunubi ne a nada Atiku a matsayin shugaban Najeriya,” kuma har gobe a kan haka Obasanjo yake,” in…

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gargadi ’yan Najeriya da cewa kada su rudu da romon bakan da abokin hamayyarsa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ke musu.

A cewar Tinubu, abin kunya da Atiku ya yi a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Kasan Najeriya a mulkin Jam’iyyar PDP ya kai makura kuma ya isa zama darasi.

Daraktan Yada Labarai na Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyanna haka ne a martaninsa ga ikirarin da Atiku ya yi cewa tun da Najeriya ta dawo kan tafarkin dimokuradiyya a 1999, babu lokacin da ’yan kasar suka fi jin dadi kamar zamanin mulkin PDP.

Amma a martanin Tinubu ta hannun Onanga, ya bayyana cewa, Atiku, “yana musu dadin baki sai ka ce zamanin mulkin nasu da aka ci bakar wahala ya fi kowane lokaci dadi a tarihin kasarmu.”

Ya ci gaba da cewa, “Muna gargadin ’yan Najeriyar kada su rudu da romon bakan Atiku da PDP ke musu a yunkurinsu na komawa kan mulki ko ana ha maza, ha mata.

“Wai jam’iyyar da ya kamata ta lullube kanta saboda abin da kunya da gwamnatinta ta yi daga 1999 zuwa 2015, ita ce ta dawo tana kokarin juya barnar da ta aikata, sai ka ce wani babban abin kwarai ta yi a tarihin kasarmu.

“Tabbas wannan kanzon kurege ne, kuma mu ba wawaye ba ne. ’Yan Najeriya ba za su rudu ba da wadannan karairayi da dan takarar da jam’iyyarsa suke tallatawa.

“Wani babban abin kunya shi ne, yadda babu ta-ido, Atiku ya fito neman kuri’ar ’yan Najeriya, duk da abin da uban gidansa, Shugaba Olusegun Obasanjo, ya rubuta a kansa a littafinsa mai suna ‘My Watch’.

“Obasanjo ya rubuta cewa babbar katobara ce, ‘zunubi ne a nada shi a matsayin shugaban Najeriya,’ kuma har gobe matsayar Obasanjo ke nan a game da Atiku.”

Tinubu ya kuma kalubalance shi kan wasu alkawuran da ya yi a gangamin yakin neman zaben PDP a Abuja, inda ya ce, “Atiku ya san cewa wannan ce damarsa ta karshe ta neman kujerar shugaban kasa”.