✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Kungiyar Marubuta ta yi sababbin shugabanni a Kano

Tukur Arab na Gidan Rediyon Muryar Najeriya ya zama Ma’aji.

Kungiyar Marubuta Labaran Wasanni ta Kasa (SWAN) reshen Jihar Kano, ta zabi sababbin shugabannin da za su ja ragamarta na tsawon shekara uku.

A jawabinsa mai sanya idanu kan zaben kuma Mataimakin Shugaban Kungiyar ta Kasa a Arewa maso Yamma, Lurwanu Idris Malikawa ya ce an bi duk dokokin da kungiyar ta shimfida wajen gudanar da zaben.

A jawabin sabon Shugaban Kungiyar Zaharaddini Sale ya sha alwashin dorawa wajen ciyar da kungiyar gaba kamar yadda sauran shugabannin kungiyar suka gabatar.

An zabi Zaharaddin Sale daga gidan Rediyon Pyramid FM a matsayin sabon Shugaban Kungiyar, yayin da Abdulgaffar Oladimeji na jaridar Sketch ya zama Sakatare, sai Aminu Halilu Tudun Wada na gidan Rediyon Freedom ya zama Mataimakin Sakatare.

Tukur Arab na Gidan Rediyon Muryar Najeriya ya zama Ma’aji shi kuma Abubakar Jibrin ya zama Mai Binciken Kudi.

An zabi Mubarak Isma’il a matsayin Mai kula da Walwalar kungiyar. Shugaban Gudanar da Zaben Aminu Kwaru ya bayyana cewa an yi waje da wasu ’yan takara da ba su cika sharudan Kungiyar SWAN ba.