✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar ’yan Najeriya mazauna Bangladesh ta yi sabbin shugabanni

Wannan ne karo na farko da aka yi zaben babu tangarda

Kungiyar ’yan Najeriya mazauna kasar Bangladesh ta gudanar da zabe inda mambobinta suka zabi wadanda da za su ci gaba da jan ragamar harkokin kungiyar.

Da yake yi wa Aminiya karin haske ta waya kan zaben wanda ya gudana a Talatar da ta gabata, Injiniya Usman Mohammad Tomsu, dan asalin Jihar Borno kuma mazaunin kasar ya ce, sun yi zaben ne domin wakilta wadanda za su shige wa ’yan Najeriya mazauna kasar gaba wajen gudanar da harkokinsu.

Ya ce wannan shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan zabe ba tare da samun wata tangarda ba sabanin zabubbukan da suka gabata.

Ya kara da cewa, babban aikin shugabannin kungiyar shi ne daukar korafe-korafen ’yan Najeriya mazauna kasar zuwa ofishin jakadancin Najeriya da ke Indiya don magance su.

Daga nan ya bayyana matsalar da ke ci musu tuwo a kwarya da cewa, “Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne, rashin ofishin jakadancin Najeriya a Bangladesh. Don haka duk matsalar da ta taso dole sai mun dangana da Indiya saboda a can ofishin jakandancin Najeriya yake.

“Zai taimaka wajen kara armashi ga zamantakewar ’yan Najeriya a kasar idan aka bude ofishin jakandancin Najeriya a Bangladesh,” inji shi.

Zauren zabe
Zauren zabe

Sabbin shugabannin kungiyar da aka zaba a zaben sun hada da: Mista Frank Jacob a matsayin shugaban kungiya, Ubom Henry Felix a matsayin Mataimakin Shugaba, Injiniya Usman Mohammad Tomsu a matsayin Sakatare Janar, Ekwueme Ngubueze a matsayin Sakataren Kudi, Chukwu Chinonye Michel P. a matsayin Ma’aji, sai kuma Okafor Kingsley C. a matsayin alkalin kungiya.