✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso ya zabi abokin takararsa

Kwankwaso ya zabi wani lauya dan Jihar Legas a matsayin abokin takararsa.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zabi wani lauya dan Jihar Legas, Barista Ladipo Johnson, a matsayin abokin takararsa a Zaben 2023.

Jam’iyyar NNPP ce ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter @nnpphqabuja1 a ranar Juma’a.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Mista Johnson tsohon dan takarar kujerar gwamnan Jihar Legas ne a jam’iyyar ANP gabanin komawarsa NNPP mai alamar kayan marmari.

Sai dai kawo yanzu babu wani tabbaci ko jam’iyyar NNPP ta zabi Mista Johnson ne a matsayin abokin takarar Kwankwaso na wucin-gadi ko kuma abokin takara ne na hakika.

A ranar 16 ga watan Yuni ne dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnann Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben badi.

Ita kuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta mika sunan wani jigon dan siyasa daga Jihar Katsina, Alhaji Kabiru Ibrahim Masari a matsayin wanda zai yi wa Asiwaju Bola Tinubu abokin takarar Shugaban Kasa na wucin gadi.

Wannan dai na zuwa ne a sakamakon rashin cimma matsaya da jam’iyyar APC ta yi bayan cikar wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayar na mika sunayen ‘yan takarar kujerar Mataimakin Shugaban Kasa.

An mika sunan Masarin ne bayan yarjejeniyar da aka yi da shi ta cewa zai janye daga matsayin abokin takara bayan an cinma matsaya kan wanda ya kamata ya zama mataimakin dan takarar Shugaban Kasa kamar yadda a sashe na 31 na Dokar Zabe ya sahale.

A ranar Juma’a ce dai wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayar na mika sunayen ‘yan takarar kujerar shugaban kasa.