✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Likitoci sun fara yajin aiki kan garkuwa da mutane

Likitoci sun shiga yajin aiki saboda garkuwa da abokan aikinsu da ’yan bindiga suka yi a Jihar Ogun

Likitoci sun tsunduma yajin aiki saboda garkuwa da wasu abokan aikinsu da ’yan bindiga suka yi.

Likitoci da malaman jinya a Jihar Ogun sun fara yajin aikin ne daga safiyar Talata domin nuna fushinsu kan yadda ’yan bindiga suka dauki sarar sace likita da malaman jinya domin karbar kudin fansa a Jihar.

“Za mu ci gaba da yajin aikin har sai an tabbatar da tsaron lafiyarmu, saboda abin da ke faruwa ya nuna ma’aikatan lafiya ba su da tabbaci game da tsaron lafiyarsu,” inji sanarwar da suka fitar.

Masu garkuwa da suka yi awon gaba da su tun ranar Laraba a kan hanyar Abeokuta zuwa Imoke na neman kudin fansa Naira miliyan 20.

A ranar Litinin kuma, an yi garkuwa da wata likita a Babbar Asibitin Ijebu Igbo a Jihar.

Kungiyoyin likitoci da sauran ma’aikatan lafiya jihar sun bayyana bacin ransu game da lamarin, inda suke zargin gwamnatin jihar da gazawa da kuma nuna halin ko-in-kula wajen ceto mambobinsu da aka yi garkuwa da su.

“Rashin yin katabus daga gwamnati wurin tattaunawa da masu garkuwar ya za ba mu da wani zabi face mu ya nuna mana cewa ba ta damu da rayuwarmu da tsaron lafiyarmu ba,” inji sanarwar da suka fitar.