✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mace ta farko ta zama shugabar Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa

Farfesa Maimuna Waziri ta doke mutum 47 da suka yi takarar neman kujerar

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa a Jihar Yobe ta amince da nadin Farfesa Maimuna Waziri a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a ranar Asabar dauke da sa hannun Shugaban Sashen Watsa Labaranta, Usar Ignatius.

Maimuna, wacce Farfesa ce a bangaren Ilimin Sinadarai za ta maye gurbin Shugaban Jami’ar mai barin gado, Farfesa Andrew Haruna, wanda wa’adin mulkinsa zai kare a farkon watan Fabrairu mai zuwa.

Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa mai barin gado, Farfesa Andrew Haruna lokacin da yake mika takardar nadi ga sabuwar shugabar makarantar, Farfesa Maimuna Waziri

Ta sami nasarar zama Shugabar Jami’ar ne bayan ta doke abokan takararta 47 a wani zazzafan zabe da ya gudana ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2021.

Sanarwar dai ta biyo bayan taron Majalisar Gudanarwar Jami’ar, wanda Uban Jami’ar Ibrahim Akuyam ya jagoranta.

Ibrahim ya ce mutum 48 ne suka fafata domin neman kujerar, aka fitar da sunayen mutum 25, aka zabi uku daga ciki ita kuma Majalisar ta zabi Farfesa Maimuna a matsayin sabuwar shugabar.

Daga nan sai Uban Jami’ar ya taya sabuwar shugabar murna tare da kiran ta da ta rungumi kowa hannu bibbiyu domin a ciyar da makarantar gaba.