✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Magidanci ya rataye matarsa a Delta

Ba a kai ga gano dalilin magidancin na kashe matar tasa ba.

Wani magidanci mai suna Taiye ya rataye matarsa, Misis Endurance har lahira a kauyen Oviorie-Ovu da ke Karamar Hukumar Ethiope ta Gabas a Jihar Delta.

Binciken Aminiya ya gano lamarin ya auku ne a karshen makon da ya gabata a Oviorie.

Wata majiya ta ce magidancin ya tsere neman mafaka a kauyen Abraka bayan da ya aikata danyen aikin.

Ya zuwa hada wannan rahoto, ba a kai ga gano takamammen dalilin da ya sa Taiye ya kashe matar tasa ba.

“’Yar uwar wanda ake zargin ya kashe marigayiyar ce ta kira ‘yan sanda aka kama shi,” in ji majiyar.

Da aka nemi jin ta bakinsa kan batun, Kwamishinan ‘Yan San Jihar, CP Ari Muhammed Ali, ya tabbatar da faruwar haka cikin wani sakon tes da ya aike wa Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Jihar, DSP Bright Edafe.