✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe matashi, sun dauke mahaifiyarsa a Jigawa

Ana fargabar wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Sabo Yusuf a yankin Kawo na Jihar Jigawa. Zahraddeen Aminuddeen wanda ke zaman Kakakin…

Ana fargabar wasu ’yan bindiga sun kashe wani matashi mai suna Sabo Yusuf a yankin Kawo na Jihar Jigawa.

Zahraddeen Aminuddeen wanda ke zaman Kakakin rundunar ’yan sandan jihar shi ne ya inganta rahoton kamar yadda manema labarai na BBC suka ruwaito.

A cewarsa, maharan sun kai hari gidansu Sabo da tsakar daren Laraba, inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da kuma wani dan uwansa.

Kakakin ya ce Sabo ya rasu ne a wani Asibitin Birnin Kudu da aka garzaya da shi bayan maharan sun harbe shi a kirji.

“Da misalin karfe 3:35 na daren Laraba ne ’yan sandan Birnin Kudu suka samu rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun far wa gidan Alhaji Abubakar mai shekara 50 a Kawo.”

“Sun harbi dansa a kirji mai suna Sabo Yusuf dan shekara 25,” a cewar Kakakin.

Ya kara da cewa, a halin yanzu dai Kwamishinan ’yan sandan jihar ya tura jami’ai rundunar yaki da maki zuwa yankin.