✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta hargitse kan nadin sabbin shugabannin marasa rinjaye

Rikici ya barke a zauren Majalisar Datttawa kan nadin sabon shugaban masara rinjaye da mai tsawatarwa

Rikici ya barke a zauren Majalisar Datttawa kan nadin sabbin shugabannin masara rinjaye a ranar Talatar nan.

An tayar da jijiyoyin wuya ne bayan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da sunayen sabon Shugaban Marasa Rinjaye da kuma Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye.

Akpabio ya sanar da sabbin shugabannin ne bayan kotu ta kwace kujerar tsohon Shugaban Marasa Rinjaye, Simon Davou Mwadkwon (PDP, Filato) da kuma Mai Tsawatarwan bangaren, Sanata Darlington Nwokocha (LP, Abia).

Kotun daukaka karar da ta kwce kujerar Mwadkwon ta ba da umarnin a gudanar da sabon zabe, ta kuma ayyana Augustin Akobundu a matsayin halastaccen wanda ya lashe kujerar da Nwokocha ke kai.

A makon jiya ne sanatocin PDP suka yi wani taro a Abuja kan cike gurbin shugabannin da kotu ta kwace kujerunsu.

Bayan taron ne Sanata Garba Maidoki (PDP, Bauchi), ya sanar cewa sun amince a ba wa yankin Arewa ta Tsakiya shugabancin marasa rinjaye.

A zaman majalisar na ranar Talata, Akpabio ya sanar da Sanata Abba Moro (PDP, Binuwa) a matsayin sabon Shugaban Marasa Rinjaye, da kuma Sanata Osita Ngwu (PDP, Inugu) a matsayin mai tsawatarwan bangaren.

Akpabio ya shaida wa majalisar cewa Sanata Abba Moro da Sanata Osita Ngwu sun samu gagarumin goyon bayan sanatocin jam’iyyun adawa, inda 41 daga cikinsu suka goyi bayan Moro, 30 suka goyi bayan Sanata Ngwu.

Sai dai kammala sanarwar tasa ke da wuya, wasu sanatoci daga kananan jam’iyyun adawa, musamman LP, suka fara bore.

Sanata Okechukwu Ezea (LP, Inugu), ya daga kara da cewa rashin ’yan jam’iyyarsa a cikin masu jagorancin bangaren marasa rinjaye ba adalci ba ne.

“Ya za a ba wa PDP kujeru uku na shugabancin marasa rinjaye? Wannan rashin adalci ne kuma ba za mu yarda ba,” in ji shi.

Hakan ne ya haifar da hargitsi a zauren Majalisar inda sanatocin LP suka ce ba za ta sabu ba a ce babu dan jam’iyyarsu a cikin shugabannin marasa rinjaye.

A yayin hayaniyar ce Sanata Tony Nwoyi (LP, Anambra) ya zargi Akpabio da yin gaban kansa wajen zaba wa marasa rinjaye wadanda za su jagorance su.

“Me zai sa ka zaba mana shugabannin marasa rinjaye? Mu bayinka ne?” in ji Nwoyi ga Shugaban Majalisar.

Sanatocin Jam’iyyar APC mai mulki sun yi ta kokarin lallashin takwarorinsu na LP, inda wasunsu suka rika zuwa ganawa da Akpabio.

Bayan dan lokaci shugaban majalisar ya yi watsi da zargin da sanatocin jam’iyyun adawan ke masa na tsoma baki a al’amuransu.

A cewarsa, shi kawai sanar da sunayen da shugabannin sanatocin jam’iyyun adawa suka mika masa ya yi, kuma ba adalci ba ne a ki yin amfani da zabin mafi yawansu.

Daga nan ya bukaci marasa rinjayen da su sasanta tsakaninsu su tabbata sun tuntubi juna kafin su kara gabatar masa da sunaye.