✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa za ta kafa hukumar mafarauta

Dokar za ta halasta wa mafarauta samar da tsaro a cikin al’umma

Majalisar Dattawa ta fara aikin kafa hukumar da za ta halasta ta kuma kula da ayyukan masu farauta a fadin Najeriya. 

Sanata Biodun Olujimi daga Jihar Ekiti ne ya gabatar da kudurin dokar mai suna: “Kudirin Dokar Mafarauta a Najeriya ta 2020 (SB. 477)”, a zauren Majalisar.

Dokar wadda aka kammala yi wa karatu na biyu za ta kawo karshen rudanin da ake fama da shi game da halascin kungiyoyin mafarauta a Najeriya.

Olujimi ya shaida wa ’yan jarida a ranar Talata cewa yin dokar zai halasta wa mafarauta samar da tsaro a cikin al’umma, tabbatar da bin doka da oda da kuma hidimta wa jama’a.