✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa za ta yi dokar hana ’yan sanda shan giya

Majalisar Dokoki ta Kasa na yunkurin samar da dokar haramta wa jami’an tsaron Najeriya shan giya da sauran kayan maye.

Majalisar Dokoki ta Kasa na yunkurin samar da dokar haramta wa jami’an tsaron Najeriya shan giya da sauran kayan maye.

Da suke muhawara kan kudirin, ’yan majalisar sun amince cewa akwai bukatar sake duba yadda ’yan sandan Najeriya ke gudanar da ayyukansu.

Kazalika sun yi Allah wadai da kisan da wani dan sanda ya yi wata lauya a Legas mai suna Omobolanle Raheem, ranar Kirsimeti.

Wannan kuduri dai ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Babajide Obanikoro mai wakiltar Jihar Legas ya gabatar na neman a binciki dan sandan da ya yi kisan, tare da gurfanar da shi a kotu, ga zauren majalisar ranar Laraba.