✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi wa makwabcinsa yankan rago saboda abinci

Wanda ake zargin ya hada baki da mahaifiyarsa wajen binne gawar a cikin dare.

Rundunar ’Yan Sanda Jihar Edo ta cafke wani matashi dan shekara 21 bisa zargin yi wa makwabcinsa mai suna Promise mai shekara 23, yankan rago bayan wata takaddama kan abinci a garin Benin.

Matasa biyun sun samu sabani kan abincin ne da rana, inda daga bisani wanda ake zargin ya kashe makwabcin nasa cikin dare.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Edo, Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce DPO na yankin ya samu bayanai game da kisan.

Ya ce, “Wanda aka kashe da wanda ake zargin suna zaune ne a gida daya, sai kwatsam wanda ake zargin ya kai masa hari a lokacin da yake barci, ya kuma yi amfani da wuka ya yi masa yan kan rago.

“Bayan ya kashe shi sai ya hada baki da mahaifiyarsa suka binne gawar a wani rami mara zurfi a cikin gidan kusa da kabarin mahaifinsa.”