✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalar Tsaro: Buhari ya gana da Gwamnoni 36 na Najeriya

Kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF ta tattauna da shugaban kasar dangane da matsalar tsaro.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya yi ganawar sirri da gwamnoni 36 na Najeriya a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnonin karkashin Kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF sun tattauna da shugaban kasar dangane da matsalar tsaro da ke ci gaba da tabarbarewa a fadin kasar.

Tun a makon da ya gabata ne gwamnonin suka yanke shawarar yin ido biyu da shugaban kasar domin tattauna wa kan dabarun da za su magance kalubale na rashin tsaro da ya addabi kasar.

Gwamnonin sun yanke shawarar hakan ne kwanaki kadan bayan kisan gillar da ’yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram suka yi wa wasu manoman shinkafa a gonakinsu a jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar Gwamnonin, Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya fidda a ranar Juma’ar da ta gabatar bayan taron kungiyar karo na 22 da aka gudanar a ranar Larabar makon jiya, ya ce kungiyar za ta goyi bayan duk wani kudiri na yi wa Rundunar ’Yan sandan kasar garambawul domin inganta tsaro a fadin kasar.

Gwamnonin sun kuma amince su mayar da hankali ga halayyar jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro bisa la’akari da zanga-zangar #EndSARS ta nuna kin jinin rundunar ’yan sanda domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.