✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaron Abuja ya jawo sabani tsakanin Wike da Sanata Ireti

Ministar Abuja, Ireti Kingibe, ta zargi Ministan Birnin, Nyesom Wike da kin sauraron ta domin tattaunawa kan matsalar tsaro

Sanatar Abuja, Ireti Kingibe, ta zargi Ministan Birnin, Nyesom Wike da kin sauraron ta domin tattaunawa kan matsalar tsaro da ke ci wa birnin tuwo a kwarya.

Ireti Kingibe ta yi ikirarin rubuta wa Wike wasiku sakonnin waya tana neman su tattauna kan hanyar da za a tunkari matsalar domin shawo kanta, amma ya yi biris da ita.

A bayan nan dai ’yan bindiga sun addabi sassan Abuja, inda suke garkuwa da mazauna domin karbar kudin fansa, inda a wasu lokuta suke wa wadanda suka sace kisan gilla.

Aminiya ta ruwaito yadda masu garkuwa da mutane suka kashe wasu mutane hudu da suka sace a wurare daban-daban a Abuja saboda rashin kawo kudin fansan da suka bukata, suka kuma kara kudin fansan zuwa Naira miliyan 100 a kan kowane mutum.

A hirar da gidan talabijin na Channels, Sanatar Ireti ta ce, “A watannin da suka gabata na ja hankalin minista (Wike) – lokacin da ya je kare kasafin kudi – kan muhimmancin sha’anin tsaro. Wannan abu ne da na shafa magana a kai.

“Gaskiya akwai rashin jituwa tsakanin Ministan Abuja da zababbun ’yan siyasa. Ni kaina na aika masa sakonni ta WhatsApp, na kuma aika masa wasiku, amma babu wanda a ciki ya amsa.

“Ni mutane suke kawo wa kokensu, wurina suke zuwa cewa babu abin da ake yi kan matsalar tsaro. Shi minista kuma a ganinsa, babu wasu zababbu a Abuja.”

A cewar Sanata Ireti, a baya da ta yi korafi kan tabarbarewar sha’anin tsaro a Abuja, sai jami’an tsaro suka rika cewa zuzuta lamarin take yi.

“A baya na ja hankalin hukumomin tsaro, amma suka ce wai zuzuta abin nake yi,” in ji Ireti Kingibe.

Amma duk da haka ta ba da tabbacin cewa nan gaba Majalisar Dattawa za ta gayyaci Ministan Abuja game da sha’anin tsaro a birnin.