✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Boko Haram da ISWAP 377 sun mika wuya

Daga cikin tubabbun har da mata da kananan yara.

Akalla mayakan Boko Haram 377 suka ajiye makamansu a yankin Arewa maso Gabas.

Tubabbun mayakan sun hada da maza 52 da mata 126, sai kuma kananan yara 199.

Ya ce, “Dakarun sun kubutar da fararen hula 47 da aka yi garkuwa da su.

“Mayakan Boko Haram da ISWAP 377, ciki har da mata da kananan yara daga sassa daban-daban a yankin sun mika wuya.

“Duka makaman da aka kwace da masu laifin da aka kama da kuma fararen hular da aka kubutar, an mika su ga hukumar da ta dace.”

Hakan ya faru ne yayin samamen da rundunar Operation Hadin Kai ta kai kan mayakan a yankin.

Daraktan yada labarai na sojoji, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja yayin taron manema labarai da suka shirya.

Jami’in ya kara da cewa, sun samu nasarar kashe wasu mayakan ISWAP yayin farmakin.

Haka nan, ya ce sun cafke ’yan bindiga 18 da masu yi musu safarar makamai 21 da ’yan leken asiri biyu daga ketare da masu garkuwa da mutane su biyar.