✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun gano sansanonin ’yan ta’adda a Abuja – Sojoji

An kuma 'yan ta'adda takwas da makamai da dama

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce ta gano sansanonin ’yan ta’adda guda biyu a mayankar Deidei da kauyen Dukpa da ke Gwagwalada a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Dakarun rundunar sun kuma kama ’yan ta’adda takwas da makamai da dama yayin wani samame da suka kai musu.

Sabon Daraktan Yada Labarai na rundunar, Manjo-Janar Musa Dan-Madami ne ya bayyana hakan a hedkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja, ranar Alhamis.

Daraktan ya kuma ce sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyar da manyan bindigogi guda uku da adduna da wukake da albarusai da kuma Tabar Wiwi mai yawa a hannun mutanen.

Idan za a iya tunawa, a ’yan makonnin da suka gabata, ’yan ta’adda sun kashe sojoji shida a yankin Bwari na Abujar, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan mazauna Babban Birnin.

Kodayake akwai rade-radin cewar mayakan kungiyar Boko Haram da na ISWAP na da sansanoni a yankin, amma sanarwar sojojin ta kara tabbatar da labarin.

Da ya juya kan sauran aikace-aikacen rundunar kuwa, Manjo-Janar Musa ya ce dakarunsu na samun gagarumar nasara a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa Gabas da Arewa ta tsakiya.