✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun lalata gonakin Tabar Wiwi 48 a Edo – NDLEA

An kama mutanen ne a cikin shekara daya

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama lalata gonakin Tabar Wiwi kimanin 48 da suka kai fadin hekta 64 a fadin Jihar Edo cikin shekara daya.

Hukumar ta kuma ce ta kama mutum  374 da suka shigo da haramtattun kwayoyi, da kuma hukunta wasu 58 a Jihar Edo a tsakankanin watan Yunin 2021 da na 2022.

Kwamandan Hukumar a Jihar, Buba Wakawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin, babban birnin Jihar Benin.

Yana jawabi ne yayin bikin ranar yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi da aka gudanar ranar Lahadi.

Buba Wakawa ya ce hukumar ta kuma ba mutum 257 da suka dogara da shan miyagun kwayoyin horon gyaran hali, da kuma sada su da iyalinsu.

Ya ce, “Mun kama mutum 384 da suka hada da maza 281 da mata 93 dauke da miyagun kwayoyin, haka kuma mun kama magungunan da aka siya ba da izinin likita ba guda 29,961, sai kuma mutane 58 da tuni an hukunta su, sai kuma wasu 76 da yanzu haka ke fuskantar tuhuma a babbar kotun tarayya”.