✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun lalata haramtattun matatun mai sama da 70 cikin mako 2 – Sojoji

An rufe matatun ne a yankin Neja Delta

Hedkwatar Tsaro ta Kasa ta ce dakarun rundunar tsaro ta Operation Delta Safe da ma wasu dakarun sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur sama da guda 70 a yankin Neja Delta cikin mako biyu.

Daraktan yada labarai na hedkwatar, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya sanar da hakan yayin jawabi ga manema labarai kan ayyukan sojojin Najeriya na mako-mako a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce dakarun sun kai farmaki daban-daban a tsawon lokacin, inda suka sami nasarar lalata haramtattun wuraren tace mai 57 a jihohin Delta da Bayelsa da Kuros Riba da kuma Ribas.

Manjo-Janar Danmadami ya kuma ce sojojin sun kwato kwalekwale na katako guda 35, tankunan adana mai guda 304 da kuma nau’rar girki guda 172 da rijijyoyin ajiye mai guda 12 da dururruka guda biyar da dai sauran kayayyaki da dama.

Daraktan ya kuma ce sojojin sun kuma kwato ganga 34,547 na danyen mai na sata da litar man dizal 650,000 da litar man fetur 5,000 da kuma ta kananzir 10,000.

Sauran kayayyakin sun hada da famfon tunkudo mai guda bakwai da motoci guda bakwai da babura guda biyar da kuma bindigu.

Ya kuma ce an kama masu fasa bututun mai mutum biyar yayin samamen.

Danmadami ya ce rundunar tsaro ta ‘Operation Dakatar Da Barawo’ ta gano tare da lalata matatun mai guda 11 da kuma tankunan karfe na adana mai guda 107 da kwalekwale na katako guda biyar. (NAN)