✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna bukatar motoci 100,000 da kwalekwale 4,200 yayin zaben 2023 — INEC

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da haka

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce tana bukatar motoci 100,000 da kwalekwale 4,200 saboda jigilar ma’aikata da kayan zabe yayin babban zaben 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin sanya hannu a kan wata yarjejeniya tsakanin kungiyar direbobi ta kasa da takwararta ta masu tuka kwalekwale a Abuja ranar Talata.

Ya ce, “Yayin babban zaben 2023, za mu bukaci jigilar ma’aikatan zabe sama da miliyan daya da kuma kayan zaben masu yawa sau biyu cikin mako biyu daga ofisoshin jihohinmu zuwa na Kananan Hukumomi.

“Daga nan kuma za a kai su mazabu 8,809 da rumfunan zabe 176,846 a fadin kasar nan.

“Saboda haka, za mu bukaci ababen hawa 100,000 da kuma akalla kwalekwale 4,200 da za a yi amfani da su a yankunan da motocin ba za su iya zuwa ba saboda ruwa.

“Wannan jan aiki ne da ya zama wajibi a yi shi nan da kwana 66, kuma muna sa ran yin hakan cikin nasara don mu ba ’yan Najeriya nagartaccen zabe,” inji Farfesa Yakubu.

Shugaban na INEC ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa mambobin kungiyoyin biyu za su tabbatar mambobinsu sun bayar da cikakken hadin kai yayin aikin.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), Alhaji Tajudeen Baruwa, ya ce a shirye suke su ga an gudanar da zaben cikin nasara.