Daily Trust Aminiya - Mutane na mamakin labarin da na rubuta –Gwarzuwar Aminiya-Trust
Dailytrust TV

Mutane na mamakin labarin da na rubuta –Gwarzuwar Aminiya-Trust

“Ranar Kin Dillanci”, labarin da Ubaida Usman ta shiga Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust da shi, ya bude ne da yadda wasu halittu masu razanarwa ke fincike ran wani shugaba dan siyasa.
Daga nan aka shiga kabari inda ake danda mashi kuda, kafin ya fito ya yi fatalwa ya garzaya Gidan Gwamnati don neman agajin iyalinsa.
A wannan hira ta bidiyo da Aminiya ta yi da ita jim kadan kafin sanar da sakamako, gwarzuwar – wacce ta zo ta uku a gasar – ta bayyana abin da ya sa labarin ya ke ba da mamaki.