✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zan fice da PDP zuwa NNPP kafin karshen wata —Kwankwaso

Kwankwaso ya tabbatar cewa zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa NNPP kafin karshen watan Maris da muke ciki

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya tabbatar cewa kafin karshen watan nan na Maris zai fice daga Jam’iyyar PDP zuwa NNPP

Kwankwaso ya shaida wa Sashen Hausa na BBC Hausa a safiyar Alhamis cewa ya yi nisa a shirinsa na komawa NNPP.

A ranar Laraba Aminiya ta ruwaito Sakataren jam’iyyar NNPP na Kasa mai barin gado, Ambasada Agbo Gilbert Major, yana cewa Kwankwaso zai dawo jam’iyyar ce tare da tafiyar siyasara ta TNM da kuma magoya bayansa.

Ya shaida wa mahalarta taron da jam’iyyar ta shirya domin tunkarar zaben 2023 cewa Kwankwaso ya jam’iyyar da tabbacin cewa zai kasance mata dan jam’iyya mai biyayya da kuma bin dokokinta.

Kafin nan, an alakanta shi da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki ko kuma kafa wata sabuwar jam’iyya.

A watan Fabrairun da ya gabata ne dai Kwankwaso da wasu manyan ’yan siyasa suka kafa sabuwar tafiyar siyasa ta TNM.

Tsohon gwamnan ya ce babu tsari a yadda ake tafiyar da jam’iyyar PDP, lamarin da ya tilasta masa tattara kayansa domin ficewa daga cikinta.

“Ban ga wani abu da APC ko PDP za su nuna wa ’yan Najeriya da za su amince su sake zabar su ba a 2023; Don haka ina ganin ya kamata a yanzu jama’a su yi tunanin zabar mu don mu ceto mutane daga halin da suke ciki.

“A 2015, mun bai wa wasu shugabancin jiha, muna tunanin za su yi abin da ya dace, amma ba tare da sanin cewa hakan ba zai haifar da wani sakamako mara kyau ba, shi ya sa muka dawo domin ceto jiharmu,” inji shi.

Amma Ambasada Agbo Gilbert Major ya ce NNPP ba za ta ba wa tsohon ministan tsaron tikitin tsayawa takarar shugaban kasa kai-tsaye ba — za ta ba wa sauran masu sha’awa damar gwada farin jininsu.

“Babu batun ba wa Kwankwaso tikitin takarar shugaban kasa kai-tsaye, kuma ya shaida mana cewa ba ya kaunar a dauka cewa ya shigo NNPP ne domin kawai ya samu tikitin takarar shguaban kasa.”

“Na san ’yan Najeriya na ta hasashe, to ina tabbatar muku cewa mun yi nisa da tattaunawa da Kwankwaso, har mun kusa kammalawa; Nan da ’yan kwanaki za mu sanar da su inda aka kwana; Amma tabbas saura kiris Kwankwaso ya sauya sheka zuwa NNPP,” a cewarsa.

A baya dai, Sanata Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda jam’iyyar PDP ta ke kokarin mayar da shi baya, duk da irin rawar da ya ke takawa a jam’iyyar.

An dade ana kai ruwa rana tsakanin Kwankwaso da bangaren tsohon ministan harkokin waje, Aminu Wali kan jagorancin PDP a Jihar Kano.

Kwankwaso ya koma PDP ne daga jam’iyyar APC bayan zaben 2015, sakamakon takun-sakar da aka rika yi tsakaninsa da wanda ya gaje shi kuma tsohon mataimakinsa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.