✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NBC ta tsawaita wa’adin biyan bashi ga kafofin labaran da ta soke lasisinsu

NBC ta kara wa kafofin watsa labaran kwanaki hudu su biya bashin da take binsu.

Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai a Najeriya (NBC) ta tsawaita wa’adin biyan bashin da ta sanya wa kafofin labaran da ta kwace wa lasisi.

A Juma’ar da ta gabata ce NBC ta kwace lasisin tashoshin talabijin da rediyo fiye da 50 kan abin da ta kira gaza biyan bashin da take binsu kuma ta ba su awa 24 su yi hakan.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, hukumar ta ce ta tsawaita wa’adin zuwa karfe 12 na Yammacin ranar Talata, 23 ga watan Agustan 2022 maimakon kwana daya, inda ta umarci su biya kudin.

“Dukkan kafofin labaran da suka gaza biyan bashinsu, ana umartar da su kulle daga ranar 23 ga Agusta, 2022,” a cewar sanarwar da Shugaban Hukumar, Balarabe Shehu Illelah ya sanya wa hannu.

Wannan dai na zuwa ne yayin da wasu kungiyoyi ciki har da Kungiyar ’Yan Jarida (NUC) suka nuna bacin ransu kan matakin da NBC ta dauka.

Kungiyoyin da suka bayyana lamarin a matsayin wanda aka dauka ba tare ga hangen nesa ba, sun ce matakin zai janyo asarar ayyukan yi ga dubban jama’ar da suka samu abun dogaro da kai a sanadiyar kafofin watsa labaran.

Daga cikin kafofin da NBC ta kwace musu lasisi akwai: gidan talabijin na AIT, Silverbird TV, Raypower FM, Rhythm FM.

Hukumar ta ce tana bin kafofin watsa labaran kudin da suka kai Naira Biliyan N2.6 na sabunta lasisi.