Daily Trust Aminiya - PSG ta sanya sharadin sayen Ronaldo
Subscribe

Cristiano Ronaldo

PSG ta sanya sharadin sayen Ronaldo

Tauraron kungiyar Juventus, Cristiano Ronaldo, na iya tafiya Paris St-Germain idan dan wasan kungiyar na Faransa, Kylian Mbappe ya yanke shawarar tafiya Real Madrid.

Kafar labaran wasanni ta Tuttorsport ta ruwaito cewa, da yiwuwar Ronaldo zai sauya sheka zuwa PSG da zarar dan wasanta Mbappe mai shekara 22 ya zabi tafiya Real Madrid a karshen kaka.

Rahotanni da ke fitowa daga birnin Turin na Italiya sun bayyana cewa, PSG tana ci gaba da lakantar halin da Ronaldo ke ciki domin ganin ya maye gurbin Mbappe a yayin da kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya nuna sha’awarsa a kan dan wasan.

Jaridar AS ta ruwaito cewa, Real Madrid na yi wa kanta kallo a matsayin kungiyar da ke gaba wajen daukar dan wasan a bazara.

Sai dai har gobe ruwa yana maganin dauda, a yayin da a yanzu babu wani dan wasa da tauraruwarsa take haskawa a Juventus tamkar ta Ronaldo mai shekara 36.

Tun bayan barin Real Madrid a shekarar 2018, Ronaldo ya jefa kwallaye 95 cikin wasanni 125 da ya bugawa Juventus.

Daga cikin dalilin da wasu manazarta kwallon kafa ke hasashen cewa Ronaldo zai sauya sheka, sun hada da yadda a halin yanzu kofin Serie A ya subuce wa Juventus bisa la’akari da yadda Inter Milan ta yi derere a saman teburin gasar da maki 12.

Haka kuma, makonni kadan da suka gabata ne FC Porto ta koro Juventus gida a gasar cin Kofin Zakarun Turai yayin karawarsu a zagayen ’yan 16.

Ronaldo wanda ke daukan albashin Fam dubu 540 duk mako a Juventus, na iya rabuwa da kungiyar bayan shafe shekara uku tare saboda yadda take fama da karancin kudi na iya ci gaba da biyan manyan ’yan wasanta.

Duk da Daraktan Wasanni na Juventus, Fabio Paratici ya dage a kan cewa kungiyar ta kudiri aniyar ci gaba da rike dan wasan, sai dai kungiyar ka iya yanke shawarar sayar da shi saboda matsananciyar bukata ta kudi take da ita.

Ronaldo na iya zama dan wasa mafi dacewar maye gurbin Mbappe a PSG matukar ya koma La Liga. A bana Ronaldo ya jefa kwallaye 32 cikin wasanni 36 da ya buga yayin da kuma Mbappe yake da kwallaye 32 cikin wasanni 38.

Ronaldo zai dace wajen cikar duk wani burin a PSG, kasancewar dan wasan ya lashe Kofin Zakarun Turai a Manchester United da Real Madrid da kuma kofunan gasar Ingila, Italiya da Spain.

More Stories