✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rasuwar Iyan Zazzau da Taliban Zazzau ta girgiza Buhari

Ya tura tawagar ministoci domin ta'aziyya ga Masarautar Zazzau

Shugaba Buhari ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar manyan jagorori biyu a Masarautar Zazzau, Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu da kuma Talban Zazzau Alhaji Abubakar Pate.

Buhari ya aike da sakon ta’aziyyar ce a ranar Juma’a ta hannun mai taimaka masa a kafafen watsa labarai, Garba Shehu, inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da za a jima ba a manta da shi ba.

“Rasuwar jiga-jigai biyu mashahurai a Masarautar Zazzau ya kada mun zuciya saboda ba a jima ba da rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.

“Ina jajantawa tare da ta’aziyya ga iyalan mamatan da Majalisar Masarautar Zazzau da Gwamnatin Jihar Kaduna tare da addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya karbi kyawawan ayyukansu, Ya sanya su cikin Aljannarsa,” inji shugaba Buhari.

Sakon ta’aziyyar ya kara da cewa tuni Sugaba Buhari ya tura tawagar  Majalisar Ministoci don zuwa Fadar Sarkin Zazzau don gabatar da ta’aziyya a madadinsa.