✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Ukraine: EU ta kakaba wa Rasha takunkumi

Kasashen Turai sun yi taron dangi bayan Rasha ta kaddamar da hari a kan Ukraine.

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta kakaba tunkumin karya tattalin arzikin  kasar Rasha, bayan dakarun Rasha sun kaddamar da hare-hare a kan kasar Ukraine.

A safiyar Alhamis EU ta bukaci Rasha ta gaggauta janye sojojinta da matakin sojin da ta dauka a kan Ukraine, sannan ta sanar da wasu karin matakan karya tattalin arzikin Rasha da kasashen EU za su dauka.

Shugabar Hukumar EU, Ursula von der Leyen, ta ce, matakan, “Za su shafi muhimman bangarorin tattalin arzikin Rasha, ta hanyar katse su daga ci gaban zamani da manyan kasuwanni mau muhimmanci ga Rasha.

Za mu gurgunta cibiyar tattalin arzikin Rasha tare da hana ta damar tafiya da zamani; Za mu kwace kadarorin Rasha da ke kasashen EU, tare da katse huldar bankunan kasar da kasuwar hada-hadar kudaden Tarayyar Turai.

“Kamar yadda muka dauki matakin a baya, har yanzu muna tare da kasashen Amurka, Birtaniya, Kanada, da kuma Japan da Australiya da sauransu a kan wanna batu.”

Matakan na zuwa ne bayan Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya umarci dakarun kasarsa da su ragargaji yankunan Ukraine da suka kutsa, yadda ya kamata.

Hotuna hare-haren da sojojin Rasha suka kai ya nuna yadda aka ragargaza gine-gine, a yayin da wasu majiyoyi ke cewa an kashe fararen hula 10 da sojoji da dama.

Tuni dai gwamnatin ta dakatar da zirga-zirgar jiyage a Yammacin kasar da ke makwabtaka da Ukraine.

Putin dai ya musanta cewa yaki ya kaddamar a kan Ukraine, yana mai kiran abin da sojojinsa ke yi da cewa wani ‘aikin soji ne na musamman.’

Putin dai na goyon bayan yankunan Doniestk da Dombass da ke neman ballewa daga Ukraine.

Shugabar Hukumar EU, Ursula von der Leyen, ta ce, miliyoyin al’ummar Rasha ba sa goyon bayan komar da hannun agogo baya da Putin yake son yi, sannan EU da al’ummar kasashen EU na tare da mutanen Ukraine kai da fata.