✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya gindaya sharadin rabuwa da Juventus

PSG ta yi wa United zarra a yarjejeniyar da suka gabatar ta neman daidaitawa da dan wasan.

Tauraron dan wasan gaba na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, zai yi kokarin rabuwa da kungiyarsa ta Juventus muddin ta gaza samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi.

Jaridar Tuttosport ta ruwaito cewa, a halin yanzu Ronaldo ya fara shirin sauya sheka zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United da ke Ingila ko kuma Paris Saint Germain da ke Faransa.

Hakan na zuwa ne sakamakon yadda Juventus take rashin kokari a gasar Serie A inda a halin yanzu take a mataki na hudu a teburin gasar da maki 66 cikin wasanni 33 da ta buga.

Ana hasashen cewa kungiyar za ta iya sauka daga wannan mataki da take kai a yanzu duba da abun kunyar da take faman yi a wasanninta na baya bayan nan.

Ronaldo mai shekara 36 ba zai so ya ci gaba da zaman dirshan a kungiyar ba ba tare da samun damar buga wasanni a gasar zakarun Turai ba a kakar wasa mai zuwa, saboda haka yake nema wa kansa mafita inda zai saurari yanayin yarjejeniyar zawarcinsa da PSG ko United za su gabatar masa.

Rahotanni sun bayyana cewa, PSG ta yi wa Manchester United zarra a yarjejeniyar da suka gabatar ta neman daidaitawa da dan wasan.