Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu | Aminiya

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu

Sheikh Khalifa bin Zayed
Sheikh Khalifa bin Zayed
    Ishaq Isma’il Musa

Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya riga mu gidan gaskiya a safiyar Juma’ar nan.

Tuni gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki 40 bayan rasuwar shugaban da ya shafe shekaru 73 a duniya.

Hakan na kunshe ne cikin wani sako da Ma’aikatar Harkokin Fadar Shugaban ta sanar a shafinta na Twitter.

Sanarwar ta ce za a sassauto da tutocin kasar sannan an dakatar da aiki a duk wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati a dukkan matakai da kuma na masu zaman kansu, wanda za su kasance a rufe har na tsawon kwanaki uku.

Sheikh Khalifa wanda ya shafe shekaru yana fama da rashin lafiya, ya dade da daina shiga harkokin yau da kullum na tafiyar da gwamnati a kasar, inda ake ganin cewa kaninsa, Yariman Dubai, Sheikh Mohammed bin Zayed ne ke tafiyar da al’amura.

Sai dai ya zuwa babu wata sanarwa dangane da wanda zai gaji kujerarsa.

Sheikh Khalifa wanda ba kasafai aka cika ganinsa yana halartar taruka ko ganin hotunansa suna yawo ba, ya gaji mulki ne a hannun mahaifinsa, wanda ya kafa Hadaddiyar Daular Larabawan a shekarar 2004.

Ya yi fama da rashin lafiyar bugun zuciyar mai hade da shanyewar barin jiki, wanda a dalilin haka ya shafe shekaru ba a ga fuskarsa a bainar jama’a ba.