Shugaban Karamar Hukuma ya gwangwaje Hakimai 5 da motoci a Kaduna | Aminiya

Shugaban Karamar Hukuma ya gwangwaje Hakimai 5 da motoci a Kaduna

    Ahmed Ali, Kafanchan

A yayin da Ciyamomi ke kukan rashin kudi, Shugaban Karamar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna, Francis Sani, ya raba wa Hakimai biyar na Karamar Hukumar kyautar motoci.

Hakiman da aka gwangwaje dai na cikin guda 12 na masarautu hudu da ake da su a fadin Karamar Hukumar.

Da yake mika motocin ga Hakiman a sakatariyar Karamar Hukumar da ke Zonkwa, Francis ya ce ya yi haka ne don ya saukaka musu zirga-zirga ganin irin muhimmancin da suke da shi a cikin al’umma da kuma goyon bayan da suke ba gwamnatin Karamar Hukumar.

Sannan ya tabbatar wa da sauran Hakiman da ba su samu ba da su ci gaba da sauraro nan gaba kadan su ma zai gwangwaje su da motocin.

Wasu daga cikin motocin da aka raba wa Hakiman

Wasu daga cikin motocin da aka raba wa Hakiman

“Sannan ina son yin kira a gareku da ku rike motocin da kyau tare da lura da su yadda ya kamata. Sauran Hakiman da ba su samu ba su yi jakuri nan gaba kadan za su ga nasu motocin.” inji shi

Da yake mayar da jawabi a madadin Hakiman da suka karbi motocin, Hakimin Madakiya, Davif Kantiok, ya jinjina wa namijin kokarin da Shugaban Karamar Hukumar ya yi tare da yaba kokari da muhimmancinsu a cikin al’umma.

Sannan ya yi alkawarin ci gaba da mara masa baya don ganin ya cim ma nasarar ciyar da Karamar Hukumar gaba.

Hakiman da aka rabawa motocin sun hada da Hakimin Madakiya a masarautar Bajju; David Kantiok, da Hakimin Gora a masarautar Atyap; Elias Usman da Hakimin Ikulu a masarautar Ikulu; Yusuf Ashafa da na Kamantan a masarautar Kamantan; Sama’ila Tawani, sai hakomin cikin garin Zango; Alhaji Idris Muhammed.