✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Portugal ya kamu da COVID-19 ana saura mako 2 zaben kasar

Yayin da ake da kasa da makonni biyu kafin babban zaben kasar Portugal, Shugaban Kasar, Marcelo Rebelo de Sousa ya kamu da cutar COVID-19.

Yayin da ake da kasa da makonni biyu kafin babban zaben kasar Portugal, Shugaban Kasar, Marcelo Rebelo de Sousa ya kamu da cutar COVID-19.

Mai kimanin shekaru 72 a duniya, Mista Marcelo dai na neman wa’adi na biyu ne a karkashin jam’iyyar PSD.

Sai dai shugaban bai nuna wasu alamu na zahiri ba daga cutar ba, duk da dai larurar tashi ta kawo tsaiko ga harkokin yakin neman zabensa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Lusa ya rawaito ranar Talata.

Ana harsashen cewa akwai yuwuwar shugaban ya kara samun nasara a zaben da za a gudanar ranar 24 ga watan Janairu.

Daga cikin ’yan takara bakwai dake neman kujerar, tuni uku suka dakatar da yakin neman zabensu saboda matakan kariya.

Zaben dai shine zai kasance na 10 tun bayan juyin-juya-halin kasar inda sojoji suka hambarar da gwamnatin kama-karya tare da dawo da ita tafarkin dimokradiyya a 1974.