✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji: Har yanzu akwai aiki babba a gabanku — Buhari

Kada mu bari makiyanmu su wargaza mana ikon mallaka da muke da shi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya hori dakarun sojin Najeriya da su kara kaimi a fagen yaki da ta’addanci saboda a cewarsa “akwai tarin aiki a gabansu.”

Shugaban ya yi kiran hakan ne yayin gabatar da jawabansa ga dakarun soji a lokacin da ya ziyarci Barikin Soji na Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A safiyar yau ta Alhamis ce Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar, inda da misalin karfe 11 da rabi sojoji da jami’an ’yan sanda suka tarbe shi a Barikin na Maimalari.

“Kada mu bari makiyanmu da masu adawa ko kuma ’yan ta’adda su wargaza mana ikon mallaka da muke da shi.

“A yayin da nake yaba wa kwazo da jarumtarku, ina kuma tunatar da ku cewa akwai nauyi babba da har yanzu yana rataye a wuyanku a dukkan kasar baki daya.

Daga bisani shugaban ya ziyarci dakarun da suka jikkata a filin daga.