✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun bindige ’yan bindiga a Kaduna

Sojoji sun yi wasu ’yan bindiga kwanton bauna inda suka kashe biyu daga cikinsu a Jihar Kaduna. Sojojin Operation Thunder Strike sun kashe ’yan bindiga…

Sojoji sun yi wasu yan bindiga kwanton bauna inda suka kashe biyu daga cikinsu a Jihar Kaduna.

Sojojin Operation Thunder Strike sun kashe ’yan bindiga biyu yayin wani kwanton baunar da suka yi cikin dare a hanyar Gwagwada zuwa Chikun  da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna. 

Aminiya ta gano cewa bayan ’yan bindigar a kan babura sun zo kusa da wurin da sojojin suke, da suka ga alamun yi mutu kwanton baunar, sai suka bude wuta a kokarinsu na wucewa. 

Duk da haka sojojin suka shawo kansu suka kashe su yayin da sauran suka arce da raunukan harbi. 

Kwamishinan Tsaro da Harkocin Cikin Gida, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa ya ce abubuwan da akwa kwato sun hdada gawarwakin, babur daya, bindiga kirar gida, wayar hannu, da tabar wiwi.

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya taya sojojin murna kan nasarar da suka yi.