✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun hallaka ‘yan biniga a Binuwai

An yi dauki ba dadi tsakanin sojoji da ’yan bindigar a wata kasuwa

Akalla muutm hudu ne aka aika lahira a wata musayar wuta da aka yi tsakanin sojoji da ’yan bindiga a Jihar Binuwai.

An harbi wasu mutum 13 a harin ’yan bindigar da ake zargin yaran shugaban mai garkuwa da mutane a Jihar, Terwase Akwaza, Gana, da sojoji suka bindige a watannin baya ne.

Yaran na Gana sun kwashinsu a hannun Dakatun Runudunar Operation Whirl Stroke (OPWS) ne a Abaji, yankin Shitile da ke Karamar Hukumar Katsina ta Jihar Binuwai.

Mazauna sun ce yaran Gana sun auka wa Abaji ne da almurun ranar Laraba, suna harbi ta duk wanda suka yi arba da shi, amma suka gamu da gamonsu a hannun sojojin da suka yi gaggawar kawo dauki, yayin da mutane ke ta gudun neman tsira.

“Motar jami’an tsaron ta kwashe gawarwakin, ba zan iya cewa ga iya yawan wadanda aka kashe ba, kuma mutane da yawa sun ji rauni,” inji wani mazaunin garin.

Shugaban Karamar Hukumar Katsina Ala, Alfred Atera, ya tabbtatar da mutuwar mutum uku, wasu 13 kuma sun ji rauni a harin da aka kai ranar kasuwar garin, Laraba da yamma.

Ya ce da zuwa maharan suka fara harbi, nan take suka kashe mutum daya suka kuma harbi wasu mutum 13.

Daga baya sojoji suka kawo dauki suka kuma bindige biyu daga cikin maharan, suka kwace makamansu.

Wasu shaidu sun ce kazamin fada da aka yi tsakanin sojojin da ’yan bindigar ya jefa mutanen garin cikin tashin hankali.

Kwamandan Rundunar Sojin ya ki amsa tambayar wakilinmu, amma mai magana da yawun ’yan sanda a jihar, DSP Catherine Anene, ta tabbatar wa Aminiya cewa an kasu mutu daya a harin da aka kai kasuwar.

Ta ce maharan sun batar da sawu ne kamar ’yan kasuwa kafin daga baya sun fara harbe-harbe, da kusan magariba, inda suka kashe mutum daya.

Ta kuma tabbatar cewa ’yan sanda da sojoji sun fatattaki maharan, da ta ce sun raunata mutum 11, zuwa cikin daji.