✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Somaliya ta haramta amfani da TikTok

Ƙasar ta ce ana amfani da shafukan wajen yada ta’addanci

Gwamnatin Somaliya ta haramta amfani da shafukan sada zumunta na TikTok da Telegram, inda ta ce ana amfani da su wajen yada ayyukan ta’addanci a kasar.

Gwamnatin ta kuma hana amfani da wata manhaja da ake amfani da ita wajen yin caca ta intanet.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsammanin sojojin kasar su kaddamar da hare-hare a kan kungiyar Al-Shabaab da ke kasar.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Sadarwa ta kasar ta fitar ranar Lahadi, gwamnatin ta umarci kamfanonin sadarwar da su datse shafukan daga ranar 24 ga watan Agusta.

Sanarwar ta ce, “A kokarinmu na hana yaki da kuma yaki da ta’addancin da ya janyo zubar da jini a Somaliya, Ministan Sadarwa ya umarci dukkan kamfanonin sadarwa da ke samar da intanet da su dakatar da shafukan TikTok da Telegram da 1XBET da ke kokarin gurbata tarbiyyar al’ummar kasarmu.”

Tun a watan Agustan bara sojojin kasar suka kaddamar da hare-hare a kan kungiyar ta Al-Shabaab da ke da alaka da Al-Qa’ida a tsakiyar kasar.

Sai dai duk da hare-haren, mayakan na Al-Shabaab na ci gaba da rike iko da sassa da dama na ƙasar inda suke kai hari kan fararen hula da ’yan siyasa da kuma sojoji.

Shugaban Kasar, Hassan Sheikh Mahmud, ya sha alwashin kakkabe dukkan ’yan ta’addan da suka addabi kasar nan ba da jimawa ba.

(AFP)