✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Super Eagles za ta lallasa Jamhuriyar Benin —Ahmed Musa

Idan muka ci wasanninmu biyu matsayinmu zai daga a matakin FIFA

Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, Ahmed Musa ya bayyana kwarin gwiwar cewa kungiyar za ta ragargaza Jamhuriyar Benin a wasansu na ranar Asabar.

Ahmed Musa ya da cewa ko kunnen doki suka yi a karawar tasu da Jamhuriyar Benin su ne da nasara, amma abin da suke so shi ne Jamhuriyar Benin ta kwashi kashinta a hannun Super Eagles.

Ya ce dalilinsu shi ne, “Idan muka ci wasanninmu biyu matsayinmu zai daga a matakin FIFA, shi ya sa ba ma tunanin muyi wasan mu tashi a kunnen doki.”

Kyaftin din ya fadi hakan ne yana mai cewa a baya sun yi kuskure a karawarsu da kasar Saliyo inda bayan sun yi mata ci hudu ta farke ta kuma kara musu.

“Kasan yadda kwallo take, sakaci kadan za ka yi sai a samu akasi, amma a yanzu mun zauna min yi wa junanmu fada, mun san a wancan lokacin mun yi kuskure, amma babu yadda za mu yi haka al’amarin kwallo yake.

“Yanzu sai dai mu yi tunanin abun da yake gaba, wato wasanninmu biyu, kamar yadda na fada ko da kunnen doki muka yi mun ketare amma ba haka muke so ba,” kamar yadda ya bayyana.

Kyaftin din ya kara da cewa a kwai zakakuran matasa a kungiyar kwalon kafar ta Super Eagle masu jini a jika, kuma ko wanne na kokari sosai a kungiyar da yake buga wa wasa.

A cewarsa, don haka suna da tabbacin nasara a wasan da za suyi a ranar Asabar da kasar  Benin a birnin Kwatano da wanda zasu yi da kasar Lesotho a Legas.

Zamu dawo Legas da wasa

A yayin wata ganawar tasu da Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, Ahmed Musa ya ce ’yan wasan za su dawo da buga akasarin wasanninsu a Jihar Legas.

Ya ce za su yi hakan ne duba da gagarumin gyaran da Gwamnan ya yi a filin wasannin jihar.

Ahmed Musa yana mika wa Gwamna Sanwo-Olu rigar kungiyar Super Eagles.

“Filin wasanni na Taslim Balogun da ke Legas daya ne daga cikin uku mafiya kyau a Nageriya.

“Kafin gyaran da Gwamnan ya yi, kusan shekaru 11 ke nan rabon kungiyar ta yin wasa a Legas, tun lokacin wasanmu da kasar Saliyo ba mu sake wasa a Legas ba, yanzu haka Gwamnan ya gyara filin.

“Mun tabbatar da haka a wasan gwajin da muka yi ranar Talata 23 ga Maris, 2021, don haka ina ganin nan gaba mafi yawan wasanninmu a Legas za mu yi su,” inji shi.