✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harbi a Kasuwar Olomore: ’Yan Arewa sun kaurace wa kasuwannin Abeokuta

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan kasuwa da leburori da ’yan acaba suka kaurace wa kasuwannin birnin Abeokuta inda suka hallara a kofar…

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan kasuwa da leburori da ’yan acaba suka kaurace wa kasuwannin birnin Abeokuta inda suka hallara a kofar fadar Sarkin Hausawan Abeokuta Alhaji Ibrahim Hassan Hassan a wani mataki nA bayyana alhininsu kan matsalolin da suke fuskanta a Jihar Ogun

Sarkin Hausawan ya shaida wa Aminiya cewa ya umarci jama’arsa su kaurace wa kasuwannin ne a ranar Litinin wadda ranar kasuwar Lafenwa da ke daura da Unguwar Hausawa ta Sabo Abeokuta, inda ya ce sun yi haka ne don nuna suna da amfani kuma suna bada gudunmawa ga ci gaban harkokin kasuwanci da na zamantakewa a jihar

Ya ce, “Makasudun wannan taro shi ne mutanenmu na fuskantar matsaloli, za ka ga ’yan kasuwarmu ana tsangwamarsu a wuraren da suke aje kayan kasuwancinsu, ana korar su, ba mu da wani matsuguni na a-zo-a-gani a kasuwannin Abeokuta, sai a bakin titi, a bakin titin nan akan zo karbar haraji, wadanda ake turowa ba mu sani ba ko gwamnati ke turosu ko kuma shugabannin kasuwa ne na yankin Iyaloja da Babaloja suna bada tikiti kullum ana karbar naira 50. A kan wannan za ka ga mai karbar haraji yana marin dan kasuwa daga nan sai matsala ta taso.”

Sarkin Hausawan ya ce,  “Yawanci rashin fahimtar harsunan juna ke janyo haka, domin akasarin ’yan kasuwarmu bakinmu  ne daga Arewa wadanda ba sa jin Yarbanci don haka muke ganin ya zama dole mu yi wannan taro domin a san yadda za a shigar da mutanenmu cikin sha’anin karbar harajin, saboda rashin jin harshe babbar matsala ce, domin wadansu mutanenmu ba sa jin Yarbanci ba su jin Ingilishi, don haka muka bada umarni kada kowane Bahaushe ya je kasuwa, domin idan muka yi fashin kwana daya za su gane amfaninmu.”

Ya ce harbin ’yan Kasuwar Olomore da ’yan sanda suka yi a makon jiya ne abin da ya sanya su suka farga domin magance matsalolin da ’yan Arewa ke fuskanta a Jihar Ogun. Ya ce Allah ne Ya kiyaye da tarzomar ta tashi bayan harbin ’yan kasuwar da ’yan sandan da ke yaki da ayyukan ’yan kungiyar asiri suka yi, a yunkurinsu na kama yaran manyan motocin da suke sauke kayan gwari da suka fito daga Arewa zuwa jihar. “Mun yi bakin kokarinmu har muka samu ikon kwantar wa jama’a hankali. ’Yan sandan sun biyo wadansu ’ya’yan kungiyar asiri ne, da suka tsere ba su samu damar kama su ba, sai suka biyo ta kasuwar suka samu yaran motocin da ke sauke kayan suna kwance a karkashin mota suna hutawa sai suka yi kansu suka kama mutum biyar. Ganin haka sai ’yan kasuwar suka nuna rashin goyon bayansu ga kamen domin ba su aikata laifin komai ba. Wannan ne ya sa jama’ar kasuwar suka ce ba za a tafi da su ba, nan hayaniya ta kaure, saukin abin akwai Shugaban Kasuwar wanda shi ne ya ce a kyale ’yan sandan su tafi da yaran, ana haka sai ’yan sandan suka fara harbin kan mai uwa da wabi, inda harsashi ya samu yaranmu biyu, Abbati Musa wanda harsashin ya goge shi a kai da Auwalu da harsashi ya same shi a kafa, dukkansu yanzu suna asibiti suna murmurewa,” inji shi.

Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Mista Kenneth Erimson ya sha alwashin binckar lamarin ya kuma taimaka da wani sashi na kudin asibiti da ake kula da wadanda suka jikkata. “Daga bisani na je ofishin ’yan sanda na Lafenwa inda aka tsare yaran motar biyar aka ba ni su, babu kuma wani laifi da aka tuhume su da aikatawa,” inji shi Sarkin Hausawan ya yi fatar mahukuntan jihar za su duba koke-kokensu.

Aminiya ta ziyarci Kasuwar Kayan Gwari ta Olomore da ke Abeokuta inda ’yan sandan suka harbi ’yan kasuwar biyu, Shugaban Kasuwar Alhaji Nuya Isiyaku ya shaida wa Aminiya cewa yana gefen gonarsa da ke karkashin gada daura da kasuwar, ya ga wadansu matasa biyu da suke kan babur wadanda su ne ’yan sandan suka biyo suna kokarin kama su, bisa zargin ’yan kungiyar asiri ne. “Koda na gifta ta gefensu dayansu ya yi min wani irin kallo na mara gaskiya, ban saurare su ba ina tafe ina waya sun bi ta jikin layin dogo can sai ga ’yan sanda sun biyo su a guje, haka ’yan sandan suka dawo ba su kama su ba. Juyowarsu ke da wuya suka kama mana yaran mota da direbobin da suka sauke mana kaya. Sai na yanke wayar da nake yi na nufi wajen da sauri na ce masu wadannan yaranmu ne direbobi ne da yaran motoci da suka sauke mana kaya yaya za ku kama su, laifin me suka yi? Sai dayansu ya ce wa direban ya ja motar su tafi da su, na ce masa a’a ya tsaya ya saurare ni, ni ne shugabansu, ’yan kasuwa ne. Ana cikin haka sai suka fara harbi, ina fada masu kada su yi harbi kasuwa ce nan, nan suka ki saurarata. To shi Abbati ya taho yana fada min cewa in yi musu magana kada su tafi da yaran nan baki ne da suka kawo mana kaya. Ashe yana cikin magana harsashi ya goge shi a kai nan na ga ya tsuguna sai jini a kansa, sai muka tallafe shi, ina cewa sun yi mana barna sai aka ce min ai sun harbi Auwalu ma a kafa,” inji shi.

Ya ce a haka suka tafi da yaran motar da direbobin, sai dai daga baya, bayan ’yan kasuwar sun nuna rashin jin dadinsu sun yi zanga-zanga ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Kenneth Ebrimson ya zo ya ba su hakuri ya lallabe su. Kuma ya je asibiti ya duba wadanda aka jikkata, ya bada Naira dubu 100 ya ce a saya musu magani, sannan ya fada wa jami’an asibitin su ba su kula, kuma ya bada umarnin a saki direbobinmu da yaransu da aka kama.

Shugaban ya ce haka ’yan sandan suke yi idan sun zo sun kama wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, sai su zuba kudin su ce sai an biya kafin su saki mutum. Ya ce a gaskiya ya kamata a duba yanayin da ’yan sanda suke aiki.

An sallamo ’yan kasuwa biyu da ’yan sandan suka harba daga asibiti ranar Litinin da ta gabata. Abbati Musa wanda harsashi ya goge shi a kai ya shaida wa Aminiya cewa “Wannan abu kaddara ne kuma Allah Ya takaita domin ga ni yanzu ina magana da ku, babu abin cewa sai godiya ga Allah, amma ’yan sandan sun yi niyyar kashe mu ne, ba don kiyayewar Allah ba da yanzu sun kashe mu a banza. Wannan shi ne halin mafi yawan ’yan sanda a yanzu, bayan nan ma sun kashe wani a Shagamu, abin da ya faru mun ga suna yunkurin kama direbobin da suka kawo mana kaya da yaransu ne sai na taso ina magana da su ’yan sandan ina fada musu cewa wadannan bakinmu ne, kaya suka kawo mana, magana kawai muke yi da su sai suka fara harbi, sun yi niyyar kashe mu ne.”

Ya ce “Asibitin da aka kai su ba su samu wata kyakkyawar kula ba, domin ba su da kwarewar aiki, duk da ’yan sanda sun ce za su dauki nauyin aikin da aka yi mana abin da suka bayar bai isa komai ba domin ’yan uwanmu ne suka rika saya mana magani, kuma dan uwana Auwalu da aka harba a kafa yanzu ya koma gida Arewa kuma har yanzu akwai harsashi a cinyarsa, kuma an gwada jininsa ya hau, yana da mata uku da ’ya’ya bakwai sannan mahaifiyarsa ta damu tana so ya koma gida ta gan shi, don haka ya tafi.”

Abbati ya yi kira ga gwamnati ta bi musu hakkinsu kuma a tabbatar an hukunta ’yan sandan da suka harbe su. Ya ce dan uwansa da aka harba a kafa ya tafi da harsashi a cinya duk da a baya an ce za a tsaya a yi aiki sai dai daga bisani sun ce in yana shan maganin da suka ba shi harsashin zai taso sama sai a matse shi ya fito. Wannan shi ne abu na biyu da ake zargin’yan sandan Jihar Ogun da aikatawa cikin wuni biyu da ya jawo musu tofin Allah-tsine inda bayan harbi a Kasuwar Olomore a ranar Juma’a, washegari Asabar suka yi sanadiyar mutuwar wani matashi dan kwallo a garin Shagamu lamarin da tada kurar da ta jawo rasuwar wadansu mutane da suka yi zanga-zangar sukar haka.