✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Leicester City ba ta fitar da rai a kan Ahmed Musa ba

Da alama kulob din Leicester City na Ingila ya nuna har yanzu bai fitar da rai daga cefano dan kwallon Najeriya da ke bugawa kulob…

Da alama kulob din Leicester City na Ingila ya nuna har yanzu bai fitar da rai daga cefano dan kwallon Najeriya da ke bugawa kulob din CSKA Moscow na Rasha Ahmed Musa ba.
Idan za a tuna, kafin a rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo a watan jiya, kulob din City ya taya Ahmed Musa a kan Fam miliyan 15.1 amma kulob din ya ki amincewa da tayin.
A halin yanzu kulob din City ya dage akan zai sake taya dan kwallon a kan Fam miliyan 18.9 kwatankwacin Naira Biliyan 8 da miliyan 170 idan aka sake bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a karshen kakar wasa ta bana.
Haka shi ma kulob din Manchester United na Ingila an ruwaito yana sha’awar dan kwallon, kuma maiyiwuwa shi ma ya sake shiga cinikin idan aka bude kasuwar cinikin ’yan kwallo a nan gaba.
Rahotanni dai sun nuna Ahmed Musa  yana sha’awar komawa Ingila don cigaba da kwallo idan ya samu damar yin haka.