✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takarar Muslimi da Musulmi shi ne zabi mafi kyau ga Najeriya —Adamu

"Tsarin dimokuradiyya ne, kowa yana da ikon ya rike ra'ayinsa. Kuma wannan hadin ’yan takarar shi ne mafi kyau ga Najeriya a yanzu," in ji…

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce tsarin da bai wa ’yan takara tikiti shi ne wanda ya fi dacewa da abin da ’yan Najeriya ke bukata a wannan lokacin.

A wata tattaunawa da Shugaban ya yi da BBC Hausa, ya ce takarar hadin Musulmi da Musulmi shi ne mafi kyau ga APC ta lashe babban zaben 2023.

Dan takarar Shugaban Kasa a APC, Bola Tinubu, ya zabi tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa — zabin da ke ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce daga wasu ’yan jam’iyyar da wasu ’yan Najeriya.

Abdullahi Adamu ya kara da cewa, “A wannan yanayi zai yi wuya a iya shawo kan al’ummar kasar kan wannan hadi saboda.

“An samu wani hali ne a kasar da ko me ka ce, akwai wadanda za su yi suka, ba za su yarda ba kuma ba yadda ka iya da su.

“Sai dai tun da ana kan tsarin dimokuradiyya ne, kowa yana da ikon ya rike ra’ayinsa. Kuma wannan hadin yan takarar shi ne mafi kyau ga Najeriya a yanzu,” in ji shi.

Adamu ya ce, duk da kalubalen tsaro da matsalar tattalin arziki ba zai hana jam’iyyar lashe zaben na 2023 ba.