✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Taliban ta haramta wa matan Afghanistan zuwa jami’a

Taliban ta ce haramcin zai fara aiki ne nan take

Gwamnatin Taliban ta sanar da haramta wa dukkan matan Afghanistan zuwa jami’o’in kasar, kamar yadda wata wasika daga Ministan Ilimi mai Zurfi ta Kasar ta sanar.

Sanarwar ta ce haramcin zai ci gaba ne har sai abin da hali ya yi, kuma ana sa ran ya fara aiki nan take.

Gwamnatin ta ce ba zai yiwu mata su ci gaba da zuwa jami’o’in ba daga yanzu, har sai abin da hali ya yi.

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa Kakakin Ma’aikatar Ilimin kasar a ranar Talata cikin sanarwar ya umarci dukkan jami’o’in gwamnati da masu zaman kansu a kasar da su dakatar da mata daga zuwa makarantun da gaggawa, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar.

Wasikar, wacce Ministan Ilimin Kasar, Neda Mohammed Nadeem ya sanya wa hannu, ta ce, “Muna sanar da ku da ku aiwatar da wannan dokar ta hana mata zuwa jami’o’i har sai abin da hali ya yi.”

Sai dai ana fargabar sabon matakin na Taliban ya jawo kakkausar suka da martani daga kungiyoyin kasa da kasa da ma kasashen ketare.

Kakakin Ma’aikatar Ilimin, Ziaullah Hashimi, wanda ya wallafa wasikar a shafinsa na Twitter ya tabbatar da sahihancinta ga kamfanonin dillancin labarai da dama, ciki har da na AFP da AP.