✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tottenham ta sallami kocinta Mourinho

Sau goma Mourinho yana shan kashi a kakar wasannin bana.

Rahotanni daga birnin Landan sun nuna cewa kungiyar Tottenham, ta sallami kocinta Jose Mourinho bayan shafe watanni 17 yana jan ragamar horas da ’yan wasa a kungiyar.

A watan Nuwambar 2019 ne Mourinho ya maye gurbin Maurio Pochettino, inda ya jagoranci kungiyar ta kare a mataki na shida a teburin gasar Firimiyar Ingila ta bara.

A yanzu haka Tottenham tana matsayi na bakwai, bayan samun maki biyu a wasanni ukun da ta buga, inda a watan Maris aka koro ta gida daga gasar Europa.

A ranar Lahadi ce Spurs za ta kara da Manchester City a wasan karshe na Kofin Carabao, wanda a baya ake kira Carling Cup.

A kakar wasannin bana, Mourinho ya sha kashi sau goma, wanda shi ne karon farko da ya taba fuskantar wannan koma baya a tarihinsa na mai horas da ’yan wasan kwallon kafa.

Akaluma sun nuna cewa, babu wata kungiyar Firimiyar Ingila ta da ga samu ta ga rashi ta fuskar samun maki kamar yadda Tottenham ta yi a bana cikin dukkanin kungiyoyi 20 da ke buga gasar.

Wasan karshe da Mourinho ya jagoranci kungiyar shi ne wanda ta yi kunnen doki  na 2-2 yayin karawarta da ta yi tsakaninta da Everton a ranar Juma’a.

Bayanai sun nuna cewa, Ryan Mason ne zai maye gurbinsa a matsayin kocin riko zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Tottenham na daya daga cikin kungiyoyi shida na Firimiyar ingila da suka sanar da kudirin shiga sabuwar gasar Turai ta Super League.