✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta kashe alkalin wasa ana tsaka da kwallon kafa a Neja

Dan wasan ya gamu da ajalinsa a tsakiyar wasan

Wani wasan kwallon kafa na sada zumunci a garin Madalla na Jihar Neja ya rikide ya koma jimami bayan tsawa ta fado wa alkalin wasa ana tsaka da fafata wasan.

Marigayin, mai suna Mustafa Ibrahim Coach 02 dai an ce daya ne daga cikin mambobin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), kuma ya gamu da ajalin ne da yammacin Talata.

Ya rasu ne yayin wasu wasanni da aka fafata a filayen makarantun Firamare da Sakandaren garin.

Wani da lamarin ya faru a kan idanunsa, Muhammed Musa, ya ce an fafata gasar ne tsakanin tawagar garin Suleja da ta Madalla, kuma lamarin ya faru ne wajen karfe 5:20, lokacin da ake hutun rabin lokaci.

“Likacin ana ruwan sama ne sai dukkan ’yan wasa da masu kallo suka tafi suka fake a azuzuwan makarantar.

“Alkalin wasan tare da mataimakansa sai suka koma cikin filin suka bukaci sauran ’yan wasan su ma su je su fake.

“Suna tsakiyar filin ne sai tsawar ta fado, nan take aka garzaya da biyu daga cikinsu asibiti, inda aka tabbatar da rasuwar Sulaiman, amma su mataimakan nasa sun farfado daga bisani.”

Wani dan uwan marigayin, wanda ya ce sunansa Ibrahim, ya ce an birne marigayin a gidansa da ke garin Suleja ranar Laraba.