✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon babban alkalin Jihar Neja, Jibrin Ndatsu ya rasu

Tsohon Babban Alkalin Jihar Neja, Mai Shari’a Jibrin Ndatsu Ndajiwo ra rasu. Ya rasu ne yana da shekaru 72 a duniya bayan ya yi fama…

Tsohon Babban Alkalin Jihar Neja, Mai Shari’a Jibrin Ndatsu Ndajiwo ra rasu.

Ya rasu ne yana da shekaru 72 a duniya bayan ya yi fama da gajeruwar jinya.

Marigayi Jibrin wanda kuma kafin rasuwarta shi ne Magajin Garin Nupe, an haife shi ne a garin Dakko da ke Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja kuma shi ne Babban Alkalin Jihar na shida.

Marigayin ya kuma taba rike mukamin shugaban hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar ta Neja.

Ya kuma yi Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta jihar a 1977, lauyan gwamnati, rajistaran babbar kotun jihar a 1985 da sauran manyan mukamai.

Ya zama Babban Alkalan jihar a shekarar 1991 ya kuma ci gaba da rike mukamin har zuwa 2013 tare da wasu mukamai da dama a bangaren shari’ar jihar.