✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsohon Shugaban PDP na Yobe da magoya bayansa 1,051 sun Koma APC

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Yobe, Alhaji Abbagana Tata, tare da magoya bayansa fiye da 1,051 sun koma jam’iyyar APC mai mulkin Jihar. Tsohon jagoran na…

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Yobe, Alhaji Abbagana Tata, tare da magoya bayansa fiye da 1,051 sun koma jam’iyyar APC mai mulkin Jihar.

Tsohon jagoran na PDP ya ce shi da dubban ’yan jam’iyyar PDP sun shiga jam’iyyar ta APC ne domin nuna godiya ga nasarorin da Gwamna Mai Mala Buni ya samu.

Ya ce, “Mun shiga jam’iyyar APC ne domin mu mara wa gwamnatin Buni baya domin gina jiharmu mai daraja. Za mu mara wa gwamnati da jam’iyyar baya a kokarin ciyar da jihar Yobe gaba.

“Ina so in tabbatar da biyayyarmu ga mai girma Gwamna Mai Mala Buni, da shugabancin jam’iyyar APC da kuma gwamnatin jihar Yobe,” Abbagana ya tabbatar.

Da yake karbar tsoffin jiga-jigan na PDP, Gwamna Buni, ya yaba wa wadanda suka sauya shekar bisa jajircewa da kaunar da suke yi wa jihar.

“Na yi farin ciki matuka da sauya sheka da kishin kasa da kuma godiya ga gwamnatin APC da kuke ciki yanzu,” in ji shi.

A cewar Gwamnan, Abbagana Tata dan siyasa ne mai bin ka’ida kuma mai kishin kasa da jihar sa wanda abin duniya ba shi ne a gabansa ba, ya bar jam’iyyarsa ga kan haka ya bar tsohuwar jam’iyyarsa.

“Saboda haka ina godiya da cewa irin wadannan ’yan siyasa masu kishin kasa sun gamsu da irin nasarorin da muka samu na shiga jam’iyyar mu ta APC.”

Ya kuma yi kira ga ’yan jam’iyyar da su kara bude wa wadanda suka fice daga wasu jam’iyyu kofa zuwa APC.

Gwamnan ya ce daga yanzu sabbin ’ya’yan jam’iyyar za su samu daidaito da dama kamar tsofaffin ’ya’yanta.