✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Valencia ta dauki Edinson Cavani

Cavani yana filin Mestella a wasan da Atletico Madrid ta lallasa Valencia.

Dan wasan kasar Uruguay Edinson Cavani, ya sanya hannu a kwantiragin shekara biyu da kungiyar Valencia.

Cavani mai shekara 35 bai samu kungiya ba tun bayan da kwantiraginsa ya kare da Manchester United a karshen kakar wasan da ta gabata.

A baya, dan wasan gaban ya taba buga wa Paris Saint Germain, Napoli da Palermo.

Cavani na filin wasan Valencia na Mestalla a lokacin da Atletico Madrid ta lallasa kungiyar da ci 1-0 a ranar Litinin a gasar La Liga.

Kungiyar ta yi nasarar lashe wasa daya ne cikin wasanninta uku na farko.