✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani sabon rikici ya yi ajalin mutum uku a Adamawa

Aminiya ta ruwaito cewa ƙura ta lafa yayin da al’amura suka ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Wani sabon rikici da ya barke a kananan hukumomin Numan da Demsa ya yi ajalin mutum uku a Jihar Adamawa.

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ya kunno kai tsakanin al’ummar Selti da Kpasham a wannan Larabar.

Tuni dai rundunar ’yan sandan ta kwantar da tarzomar kuma ƙura ta lafa yayin da al’amura suka ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan ’Yan sandan jihar, Dankombo Morris, ya jagoranci tawagar jami’ansa zuwa sintiri a yankin da lamarin ya faru.

Sai dai duk da haka, rundunar ’yan sandan ta ce ta tsunduma cikin bincike domin gano duk masu hannu a aika-aikar.

CP Dorris ya gargadi mazauna da su ƙauracewa shiga duk wata tarzoma sannan su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma roki jama’a da su kai rahoton duk wani mutum da suka yi zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko lambar gaggawa, wadanda suka hada da 08089671313 da 08034037570.