✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasoson kayan abinci: Gwamnatin Adamawa ta sassauta dokar hana fita

Yanzu dokar ta koma 6 na yamma zuwa 6 na safe

Gwamnatin Jihar Adamawa ta sanar da sassauta dokar hana fitar da ta sanya ta sa’o’i 24 a Kananan Hukumominta 21, bayan wasoson kayan abincin da aka yi a rumbunan gwamnati da ke Jihar.

A ranar Lahadi ce dai rahotanni suka bayyana yadda wasu bata-gari suka rika farfasa rumbunan gwamnati a Yola, babban birnin jihar, inda suka rika dibar kayan abinci da na masarufi suna guduwa da su.

Amma a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Gwamna Ahmadu Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya fitar ranar Litinin, ya ce a yanzu dokar ta koma daga 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Sanarwar ta ce sassauta dokar ya biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin tsaro na jihar da jami’an gwamnati, wacce Mataimakin Gwamnan Jihar, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ya jagoranta cikin dare.

Sanarwar ta kuma ce bayan sassauta dokar, jami’an tsaro za su ci gaba da sintiri don tabbatar da cewa an bi umarnin na gwamnati sannan bata-garin ba su sake kawo wa zaman lafiyar jihar tarnaki ba.

Daga nan sai gwamnatin ta shawarci iyaye da su kai ’ya’yansu makaranta da safe sannan wuraren kasuwancinsu ba tare da fargaba sannan su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai.

Mataimakin Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ba za ta zauna ta zuba ido bata-gari su ci gaba da kassara jihar ba.