✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Amare Suka Mai Da Ankon Bikinsu Hanyar Tara Kuɗaɗe

Ƙawayen amarya na yawan korafi a duk lokacin da suka ji labarin kawar su za ta yi aure kuma lokaci ya matso kusa, ba wai…

More Podcasts

Ƙawayen amarya na yawan korafi a duk lokacin da suka ji labarin kawar su za ta yi aure kuma lokaci ya matso kusa, ba wai dan ba su son ta yi ba, aa sai dan tunani da zura ido domin ganin samfurin ankon da za a fitar.

Wasu amaren kan tsuga kudi a kan ankon bikinsu kuma su tilasta kawaye a lalai tilas sai sun siya a hannun su, baki isa kije kasuwa ki siya ba, idan ma kin samu din toh lallai wannan kulli watakila zai kasance zuciyar amarya har tsawon lokaci.

Shirin Daga Laraba ya duba yadda wasu amaren suke mai da ankon bikinsu hanyar tara kuɗaɗe in za su yi aure.

Domin sauraren shirin, latsa nan