✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kin karbar mara lafiya a asibiti ya ta da kura

Zargin asibitin gwamnati da kin karbar wani wanda aka kade da mota ya bar baya da kura.

An tayar da jijiyoyin wuya kan zargin kin karbar wani wanda mota ta kade bayan da wata baiwar Allah ta taimaka ta kai shi Asibitin Maitama da ke Abuja.

Bidiyon lamarin da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna cacar baki tsakanin matar da jami’an asibitin na Maitama saboda a cewarta, sun ki karbar mara lafiyan da aka dauko shi jina-jina.

“Na zo wucewa a kan babbar hanya, a daidai Mabushi na ga wannan bawan Allan wani ya kade shi ya gudu. Na kawo shi asibiti kuma sun ki su karbe shi, na yi magana DPO ya ce yana hanya, amma wai sun ce sai dai a kai shi Asibitin Kasa,” injita a bidiyon.

Matar ta rika daukar bidiyon domin nuna yadda ta fusata bayan jami’an sun nemi ta wuce da mutumin zuwa Asibitin Kasa, ta kuma kekashe kasa cewa dole sai an karbe shi a Asibitin na  Maitama, tana zargin an yi watsi da mutumin ne saboda ba shi da uwa a gindin murhu.

“Asibitin ma sai mai gata ake dauka ba kowa ake dauka ba,” inji ta a da ta dauka, amma ba ta bayyana kanta ba.

An tayar da jijiyoyin wuya

Bayan tayar da jijiyoyin wuyan ne jami’an asibitin suka amince suka karbi maralafiyan mai suna, George Imohimi, wanda a halin yanzu yake samun sauki.

Babba Likitan Asibitin, Dokta Imuentinyan Igbinovia, ya ce an kwantar da mara lafiyan a bangaren aikin gaggawan asibitin inda a yanzu yake samun sauki.

“Ranar Litinin misalin karfe takwas na safe, an kawo wasu da suka yi hatsari, ma’aikata na kula da su, sai ni ma na shiga duba su. Bayan kamar minti 30 sai aka shigo da wani, shi ma suka tafi su fara duba shi.

“Abin takaicin shi ne an samu musayar yawu tsakanin wadanda suka kawo shi da jami’an karbar masu neman kulawar gaggawa, amma na shiga tsakani na kwantar da kurar na kuma yi magana da matar da ta kawo wanda ya yi hatsarin.

shin kurar ta lafa?

“Nan take aka dauko gadon daukar marasa lafiya aka kai shi sashen ba da kulawar gaggawa. Bayan an ba shi gado an dauki bayanansa, sai na yi magana da Babban Jami’in ’Yan Sandan yankin.

“Matar ta ta kawo shi tana ganin ya kamata mu gaggauta ba shi kulawa, amma na yi mata bayani.

“A iya sani ne an daidaita, an ba wa mara lafiyan gado yana kuma samun sauki.

“Daga baya kuma sai muka ga ana ta turo mana sako ta shafukan sada zumunta.

“Amma ina tabbatar wa al’umma cewa Asibitin Maitama a shirye yake domin kula da marasa lafiya, kamar yadda kuke gani, kullum sai mutane masu yawan gaske sun zo ganin likita,” inji shi.

Za mu hukunta ma’aikata —FCTA

Mukaddashin Sakataren Sashen Lafiya da Walwalar Al’umma a Hukumar Kula da Birnin Taraya FCTA, Dokta Muhammed Kawu, ya ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin, domin hukunta masu laifi.

Ya ce yin hakan shi ne matakin da ya dace da masu neman yin makarkashiya ga kokarin hukumar na samar da managarcin kiwon lafiya.

A lokacin da ya ziyarci asibitin domin duba mara lafiyan, Kawu ya ce duk ma’aikacin da ka samu da laifin sakaci da aiki zai yaba wa aya zaki.

A cewarsa, wajibi ne a kan kowace cibiyar lafiyar gwamnati ta karbi wanda ya yi hatsari ta fara kula da shi kafin cika wasu ka’idoji.

“FCTA ta damu shi ya sa Minista ya turo ni in zo in ga abin da yake faruwa in kuma shawo kan lamarin.

“Mun ga bidiyon abin da ya faru kuma muna zurfafa bincike a kai.

“Muna tabbatar wa ’yan Najeriya, musamman mazauna Abuja cewa wuraren gwamnati an yi su ne domin jama’a, saboda haka kowa yana da ’yancin zuwa kowane asibiti a duba lafiyarsa,” inji shi.