✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda likitoci mata da miji suka rasu a gobara a Maiduguri

Dokta Auta ya kama da wuta yayin da yake kokarin ceto matarsa Dokta Amina, inda cikin gaggawa aka kai su sashin ba da agajin gaggawa…

Wata gobara ta hallaka wasu likitoci ma’aurata, Dokta Auta Gidado da matarsa, Dokta Amina Ahmad da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar  Maiduguri da ke Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Lahadi a gidansu da ke Titin  Legas a birnin Maduguri.

Iyalan mamatan sun bayyana mana cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

Sai dai suna zargin fetur ne ya haddasa ta, kuma daga yanayin raunukan, Dokta Auta ya kama da wuta yayin da yake kokarin ceto matarsa Dokta Amina, inda cikin gaggawa aka kai su sashin ba da agajin gaggawa na asibitin jami’ar.

Wata majiya ta bayyana cewa Dokta Auta ne ya fara rasuwa ranar Talata, kafin matar tasa, Dokta Amina ta bi bayansa ranar Laraba.

An kuma  yi jana’izarsu an binne su, kamar yadda Musulinci ya tanada.

Da yake tabbatar mana da faruwar lamarin, Shugaban Kungiyar Kwararrun Likitoci Reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, Dokta Abdullahi Usman, ya ce yana cikin alhinin rashin wadannan jajirtattun likitocin, tare da sauran ma’aikatan Asibitin.

A karshe ya yi musu addu’ar Samun rahamar Ubangiji, da fatan mutuwar ta zama hutu gare su.