✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ma’aikacin jami’a ya rataye kansa

Ya rataye kansa bayan aike wa iyalansa sako game da 'kuncin rayuwar da yake ciki'

Ana zargin wani ma’aikacin Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife a Jihar Osun, Fisayo Oyeniyi, ya kashe kansa sakamakon bakin ciki.

Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar, Abiodun Olanrewaju, ya tabbatar da Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce marigayin ya shaida wa wasu abokan aikinsa cewa ya gaji da rayuwar da yake ciki.

Iyayen daliban Kaduna na rokon a tattauna da ’yan bindiga

Da misalin karfe 1:16 na rana ranar Alhamis ne lamarin ya faru da Oyeniyi, wanda jami’in tsaro ne jami’ar kafin rasuwarsa.

An gano marigayin ya aike da wasika ga mahaifiyarsa, ’ya’yansa mata, cewa ba shi da sha’awar ci gaba da rayuwa, saboda halin kunci da yake ciki.

Jami’in ya ce Oyeniyi ya rataye kansa ne, bayan aike da wasika ga iyalan nasa.

Ya kara da cewa marigayin bai bar abokan aikinsa sun zargi wani abu game da halin da yake ciki ba, awanni hudu bayan aika sakon waya, aka samu gawarsa ya rataye kansa a dakinsa da igiya.

Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta mika ta’aziyya tare da jajanta wa iyalan marigayin.